Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Sayyidah Ummul-Banin, matar Amiral Mu'minin Ali (AS) Abar kaunarsa kuma mahaifiyar manyan shahidai huɗu na Karbala (Sayyid Abbas (AS), Abdullah, Jafar, da Uthman), tana ɗaya daga cikin mata mafi shahara a tarihin Musulunci. Sunanta na gaskiya shine "Fatima", amma bayan ta auri Imam Ali (AS), saboda girmamawa ga Sayyidah Zahra (AS) kuma don kada a ambaci sunan "Fatima" a gidan, yana kiran ta da "Ummul banin" (mahaifiyar 'ya'ya maza). Wannan shine alamar farko ta ladabi da tawali'u na ta.
1. Ladabi Maras Misali Na Sayyidah Ummul-Banin
- Ladabi Da Girmamawarta Ga Sayidah Zahra (AS)
Lokacin da ta shiga gidan Imam Ali (AS), sai ta ce wa Hasnain (AS): "Ni baiwarku ce, zan yi duk abin da ka umarce ni." Kuma ba ta taɓa sanya kanta kusa da Sayyidah Zahra (AS), mahaifiyar Imam Hassan da Imam Husain (AS) ba. Ko bayan shahadar Sayyidah Zahra As. Kullum tana cewa: "Hasan da Husaini 'ya'yan Fatima ne" kuma tana kiransu da "Sayyidi" (Shugabana)
- Ladabinta Ga Imam Ali (AS)
Lokacin da Imam Ali (AS) ya zo neman aurenta, Ummul-Banin ta ce: "Ina da 'ya'ya maza huɗu, idan ka yarda zaka karbe su, za ka so su a matsayin 'ya'yanka to?" Wannan magana ta nuna kulawa da ladabinta wajen kare haƙƙin 'ya'yanta da makomar iyali.
- Ladabinta A Cikin Makoki
Bayan shahadar Karbala, Sayyidah Ummul-Banin ta kasance tana zuwa makabartar Baqi'ah kowace rana ta yi wa 'ya'yanta addu'o'i, da wakem jajantawa musamman ga Sayyid Aba Abdillah (AS). Waƙoƙin juyayinta sun kasance na ban tausayi da kona zuciya har ya kai ga ana cewa Marwan ibn Hakam (wanda maƙiyin Ahlul-Bait ne) yana yin kuka idan ya ji muryar kukanta. Amma ba ta taɓa ambaton sunan ɗaya daga cikin 'ya'yanta a cikin wakokin ta ba.
Kullum tana cewa: "Ya kai wanda ka ga Abbas yana mai kai hari da hujumi ga rundunar abokan gaba, alhali a bayansa akwai jarumai 'ya'yan ɗan'uwansa...". Wannan shine mafi girman ladabi da rashin son kai har ma a cikin mawuyacin hali, ba ta ambaci sunayen 'ya'yanta ba, don kada a yi batanci ga sunan Imam Husain (a.s.) a boye.
2. Renon 'Ya'yanta Da Tarbiyyar Da Ta Ba Su; Abin Koyi Maras Misali
Sayyidah Ummul-Banin ta yi nasara sosai wajen reno da tarbiyar 'ya'yanta hudu har ya zamo dukkansu hudun sun samu babban matsayin shahada a Karbala, kuma musamman Sayyid Abbas (a.s.) ya shahara da "Qamar Bani Hashim", "Saqiyl Karbala", da "Babul-Hawaij".
Muhimman abubuwan koyi da suka ɗauke a tarbiyyar da ta bawa yaranta:
- Ƙarfafa fahimtar 'yan'uwanta da biyayya ga Imamin zamaninsu
Tun daga yarinta take koyawa 'ya'yanta cewa Imam Husain (AS) babban ɗan'uwansu ne kuma Imam kuma ya kamata su sadaukar da rayukansu a gare shi. Lokacin da aka bar Sayyid Abbas (AS) ya nemi fagen daga a Karbala, ya ce: "Muddin ɗan'uwana Husain yana raye, ba lokacin shahada ta ba ne." Wannan jumla ita ke nuna irin sakamakon renon uwa wadda ta dasa himma da biyayya ga riƙon amana a cikin zukatan 'ya'yanta.
- Koyar da Jarumtaka Tare Da da Ladabi
Da wannan jarumtaka da tsoro, Sayyid Abbas (AS) ya kasance mai ladabi a gaban Imam Husain (AS) har bai taɓa kallon idanun ɗan'uwansa kai tsaye ba kuma koyaushe yana zaune ƙasa kaɗan gareshi. Ya koyi wannan babban ladabi daga mahaifiyarsa ne.
- Imani Mai Zurfi Da Tawakkali
Lokacin da aka gaya mata cewa 'ya'yanta huɗu sun yi shahada, sai ta ce: "Ka faɗa minn Meta samu Husain!" Kuma lokacin da suka gaya mata cewa Imam Husseiin (AS) shi ma ya yi shahada, sai ya ce: "Kun Tunbuke Tsokar Jikina, Dukkan Fatana Akan Husain Ne." Amma, da cikakken haƙuri da biyayya, ta ce: "Ya Allah! Na gode maka da ka ba ni 'ya'ya maza huɗu kuma ka karbe su a tafarkinka". Wannan imani da gamsuwa su ne abin da ke cikin 'ya'yanta.
3. Me Ya Sa Ummul-Banin Ta Zamo Abar Koyi A Yau?
- A cikin duniyar da iyaye mata da yawa ke tunani kawai game da samun nasarar duniya ta 'ya'yansu, amma ita Ummul-Banin ta koya mana cewa mafi girman darajar uwa ita ce 'ya'yanta su mutu a tafarkin Allah da bin sawun Imamin zamanin su.
- A lokacin da ladabi da girmamawa ga manya, musamman Ahlul-Bayti, suka ragu da karanci, mu'amalar Ummul-Banin ga Imam Hasan da Imam Husain (AS) ta zamo itace mafi kyawun darasi.
- A lokacin da haƙuri da wahalar jurewa suka zama da wahala, haƙurin Ummul-Banin bayan shahadar 'ya'yanta huɗu da Imam Husain (AS) ya zamo hasken shiriya garemu.
- A zamanin da biyayya ga shugabancin addini da kuma manufofin Allah suka ragu, cikakken sadaukarwar 'ya'yan Ummul-Banin ga Imam Husain (AS) cikakken misali ne.
Sayyidah Ummul-Banin ta kirayemu ga:
- Rayar da ladabi da soyayya ga Ahlul-Bayti a gidajenmu.
- Renon 'ya'yanmu ta yadda idan ya zama dole, za su sadaukar da rayukansu don imaninsu ba tare da wani jinkiri ba.
- A cikin baƙin ciki da wahala, kamar ita, ya kamata mu dogara ga Allah mu yi haƙuri.
Ziyarar da ake karantawa a gare ta tazo da kyakkyawan magana a ƙarshe da ke cewa:
«السَّلامُ عَلَیْکِ یَا فَاطِمَةَ بِنْتَ حِزَامٍ، السَّلامُ عَلَیْکِ یَا أُمَّ الْبَنِینَ، السَّلامُ عَلَیْکِ یَا مَنْ وَهَبْتِ أَوْلادَکِ الأَرْبَعَةَ لِلْحُسَیْنِ(ع)...»
Your Comment